Ƙungiyar Hezbollah ta fara janye mayaƙanta daga kudancin Lebanon
Hausa

Ƙungiyar Hezbollah ta fara janye mayaƙanta daga kudancin Lebanon

AP24332380000744 G

Ɗan majalisar Lebanon kuma ɗan Hezbollah Hassan Fadlallah, ya ce ƙungiyar tana baiwa rundunar sojin ƙasar ta Lebanon haɗin kai wajen janye mayaƙanta daga kudancin ƙasar, don bai wa sojojin damar maye gurabensu a yankin, kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wutar da Isra’ila ta amince da ita ta buƙata.

Fadlallah ya ƙara da cewar dama can ƙungiyar Hezbollah ba ta ta wata takamaiman sansani ko makamai da ta girke a kudancin Lebanon, kasancewar ta matsayin rundunar yaƙin sunƙuru saɓanin zama wani ɓangare na sojojin ƙasar.

Ɗan Majalisar yayi waɗannan kalaman ne, a daidai lokacin da rundunar sojin Lebanon ta sanar da fara ƙara yawan dakarunta a kudancin ƙasar, a yayin da dubun dubatar mutanen da suka tsere ke komawa gidajensu bayan da aka ƙulla yarjejeniya tsagaita wuta tsakanin Hezbollah da Isra’ila, watanni biyu bayan ɓarkewar yaƙin tsakanin ɓangarorin biyu.

Rundunar sojin Lebanon ta ce tana aikin tabbatar da tsaro a yankin kudanciin ƙasar ne tare da haɗin gwiwar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke girke a ƙasar.

Zuwa jiya Laraba, mutane dubu 3 da 823 gwamnatin Lebanon ta ce an kashe, bayan hare-haren da aka riƙa kaiwa tsakanin Hezbollah da Isra’ila daga watan Oktoban shekarar bara, sai dai akasarin mutanen sun rasa rayukansu ne, a ƴan makwannin da suka gabata, bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *