Politics

Mataimakin Gwamna Yusuf yayi murabus, ya koma APC

Mai Kadama 720x430

Mai Kadama 720x430

Abdulrahman Muhammad Sulaiman wanda aka fi sani da Mai-Kadama babban mataimaki na musamman ga Abba Yusuf gwamnan jihar Kano ya yi murabus daga mukaminsa.

Mai-Kadama ya kuma fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.

Dan siyasar wanda shi ne SSA ga gwamnan kan harkokin kasuwanci, ya bayyana sauya shekarsa ne a ranar Laraba a Abuja, bayan wata ganawa da Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Karin Wani Labarin: Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 16, ta lalata gidaje 3,936 a Jigawa

Mai-Kadama ya rike mukamai da dama kafin ya sauya sheka, ciki har da jagorantar tafiyar Kwankwasiyya a jihar Filato.

Hakazalika, ya kasance shugaban kungiyar G-6 a jihar Kano.

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Jibrin ya ce Mai-Kadama ya koma jam’iyyar APC ne domin ciyar da shugabanci nagari da kuma habaka ci gaba.

Sanarwar ta ce, “Yau Mai Kadama Kwankwasiyya yana gidana da ke Abuja, inda ya jefar da jar hula ya koma babbar jam’iyyar siyasa a Afirka, APC.

Karin Wani labarin: Ƴan mata uku sun mutu a ruwa yayin zuwa yanko ciyawa a Jigawa

“Da sauya shekar jam’iyya ya bayyana cewa shi ne Mai Kadama Maliya. Dan siyasar ya kuma bayyana murabus dinsa a matsayin babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan harkokin kasuwanci II.

“Mai Kadama ya kuma bayyana yin murabus daga mukaminsa na jagoran Kwankwasiyya na jihar Filato, jagoran G-6 na jihar Kano kuma shugaban Kwankwasiyya Akasa A Tsare na kasa domin ya bi sahun mu domin inganta shugabanci na gari, da gaggauta ci gaban kasa baki daya.”

“Sabon Mai Kadama Maliya ya yi kira ga ’yan uwansa matasa ‘yan siyasa da su shigo cikin wannan gagarumin yunkuri na mu don isar da dimokuradiyya ga al’ummarmu.

“Kamar yadda na fada a baya, jam’iyyarmu ta APC, ita ce jam’iyya daya tilo da ta himmatu wajen inganta rayuwar al’ummarmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version